1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Harin Rasha ya halaka mutane 14 a Ukraine

Suleiman Babayo MAB
March 15, 2024

Yayin da Rasha take ci gaba da kaddamar da kusten kan Ukraine wani harin na Rasha da makamai masu linzami ya halaka mutane 14 a garin Odesa na kusancin kasar Ukraine tare da lalata abubuwan jin dadin rayuwar mutane.

https://p.dw.com/p/4deAt
Kutsen Rasha kan Ukraine
Kutsen Rasha kan UkraineHoto: Ukrainian Emergency Service Office/AP Photo/picture alliance

Wani harin da Rasha ta kaddamar da makamai masu linzami ya halaka mutane 14  a garin Odesa na kudancin kasar Ukraine, kana wasu mutane kimanin 20 suka jikata kamar yadda masu aikin agajin gaggawa suka tabbatar a wannan Jumma'a.

Galibin makaman da aka harba sun fadi kan gidajen fararen hula abin da ya haifar lalata motoci da da bututun kai gas gidaje. Fiye da shekaru biyu da suka gabata kasar ta Rasha ta kaddamar da kutse kan kasar Ukraine lamarin da ya haifar da martani daga bangarorin daban-daban musamman manyan kasashe na Yammacin Duniya da suka dauki matakin taimakon Ukraine fita daga wannan kangi.