Hari kan cibiyoyin mai na ′yan kungiyar IS | Labarai | DW | 26.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari kan cibiyoyin mai na 'yan kungiyar IS

An yi luguden wuta kan wuraren da 'yan jihadin na kungiyar IS ke amfani da su wajen fidda danyen mai a gabashin Siriya.

Rahotanni na cewar an kai hare-haren ne da safiyar yau a Deir el-Zour baya kuma ga wani hari da aka kai a hedikwatar kungiyar ta IS a garin Mayadeen da wasu wuraren da 'yan kungiyar ke rike da su a wajen birnin Hassakeh da ke arewa maso gabashin kasar daura da iyakarta da Iraki.

Kungiyar nan ta Syrian Observatory for Human Rights da ke sanya idanu kan kare hakkin dan Adam a Siriyan ta ce hare-haren da Amirkan ta jagoranta a jiya da kuma safiyar yau sun hallaka 'yan IS da dama sai dai ba ta tantance yawan wanda suka rasu ba.

Kungiyar dai ta ce tana ganin wannan hare-hare kan cibiyoyin man da ke hannun 'yan tawayen za su yi nakasu babba garesu, kasancewar hakan zai sa su samu kalubale na samun kudaden da suke tafiyar da aiyyukansu.