1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a masallacin 'yan Shi'a a Saudiyya

Yusuf BalaMay 22, 2015

Wasu kafafen yada labarai a gabashin kasar ta Saudiyya na bayyana hotunan mutane da suka sami raunika jina-jina, inda ake garzaya da su asibiti.

https://p.dw.com/p/1FUMW
Jemen Bombenanschlag in einer Moschee in Sanaa
Hoto: Reuters/Khaled Abdullah

Wani harin kunar bakin wake da aka kai masallacin 'yan Shi'a a gabashin kasar Saudiyya a ranar Juma'an nan ya yi sanadin mutuwar mutane da dama kamar yadda mahukunta da wasu 'yan fafautika suka bayyana.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Saudiyya ta bayyana cewa an kai wannan babban hari ne a masallacin Kudeih da ke zama a lardin Qatif matattara ga 'yan shi'a lokacin gabatar da ibadarsu ta ranar Juma'a.

Wani dan fafutika ya bayyana cewa akwai da dama da suka rasu wasu kuma suka jikkata inda wasu kafafen yada labarai da ke gabashin kasar ta Saudiyya ke bayyana hotunan mutane da suka sami raunika jina-jina.

A cewar wannan dan fafutika wani asibiti da ake kira Qatif ya bukaci al'umma da su gaggauta bayar da gudun mawar jini inda kuma ya kira ma'aikata da ke hutu a wannan lokaci su gaggauta komawa aiki a yau dan bada gudun mawar da ta dace ga wadanda suka jikkata.