Hari a kan wata cibiya ta ′yan gudun hijira a Nijar | Labarai | DW | 11.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a kan wata cibiya ta 'yan gudun hijira a Nijar

Akalla farar hula guda biyu a aka kashe 'yan gudun hijira kana aka jikkata wasu da dama a wani harin da wasu 'yan bindigar suka kai a sansanin 'yan gun hijira na Ayorou da ke a yammacin Nijar.

Magajin garin Ayorou Zakaria Oumarou ya tabbatar da harin, wanda ya ce ya afku a ranar Asabar da misalin karfe 11 na dare a wata cibiyar 'yan gudun hijira ta MDD da ke kunshe da 'yan gudun hijira na Mali.Cibiyar 'yan gudun hijira na Tabareybarey wanda ke da nisan kilomita goma daga garin Ayorou da ke a cikin Nijar na dauke da 'yan gudun hijira na Mali kimami dubu goma wadanda suka fice daga Malin tun lokacin da 'yan tawaye abzinawa suka kwace yankin arewacin kasar.