Hare-haren kunar bakin wake sun hallaka mutane hudu a Kameru | Labarai | DW | 02.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren kunar bakin wake sun hallaka mutane hudu a Kameru

Sojojin Kameru sun hallaka kimanin 'yan Boko Haram 100 tare da kwato mutane 900 da ake garkuwa da su, yayin da wasi harin ya hallaka mutane hudu a yankin arewacin kasar.

Kimanin mutane hudu sun hallaka sakamakon hare-haren kunar bakin wake guda biyu a yankin arewacin kasar Kameru da ake dangantawa da tsagerun kungiyar Boko Haram na Najeriya masu dauke da makamai. Kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito cewa akwai maharan biyu a a cikin wadanda suka hallaka abin da ya janyo adadin mutanen da suka mutu zuwa shida.

A wani labarin sojojin kasar ta Kameru sun hallaka mayakan Boko Haram kimanin 100 tare da kwato mutane 900 da ake garkuwa da su, kamar yadda wata sanarwa ta Joseph Beti Assomo ministan tsaro ke cewa, kuma sojojin sun kwato mutanen kusa da iyaka da Najeriya, lokacin da dakarun kasar ta Kameru na musamman suka kaddamar da farmaki cikin karshen watan jiya na Nuwamba.