Har yanzu ba a gano daruruwan mutane ba mako guda bayan turmutsitsi wajen aikin Hajji | Labarai | DW | 01.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Har yanzu ba a gano daruruwan mutane ba mako guda bayan turmutsitsi wajen aikin Hajji

An samu mabanbanta alkalumma tsakanin Saudiyya da kasashe 23 da suka rasa Alhazansu a turereniyar da ta auku kusa da garin Mina.

A wannan Alhamis wato mako guda bayan aukuwar turereniyar nan da ta yi sanadiyyar rayukan daruruwan mutane yayin aikin Hajji, har yanzu ba a gano wasu daruruwan mutane ba. Alkalumman da daidaikun kasashen da abin ya shafe suka bayar, sun haura wadanda hukumomin Saudiyya suka bayar. Saudiyya dai ta ce yawan wadanda suka rasu ya kai mutum 769 sannan 934 sun jikkata lokacin hatsarin a kusa da Mina. Amma alkalumman da ke fitowa daga hukumomin kasashe 23 sun ce yawan mutanen ya haura 940. Sannan wasu 600 sun bata. Iran wadda ta dora laifin aukuwar turereniyar kan kasar Saudiyya, ta fi yawan Mahajjata da suka rasu a turmutsitsin inda yawansu ya haura 460.