1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hanyar sadarwa ta intanet a wasu motocin tasi a Legas

Sam Olukoya/ KSSeptember 9, 2015

Mazauna birnin na Legas da ke kudu maso yammacin Tarayyar Najeriya sun sami wata damar amfana da kayayyakin yanar gizo a motocin haya kyauta.

https://p.dw.com/p/1GTfu
Still DW Beitrag Internetzugang in Metro Taxi Lagos
Hoto: DW

Wannan dai wata muhimmiyar dama ce da motocin haya na tasi a birnin suka samar don amfanar kwastamominsu kyauta ba tare da biyan ko sisi ba. Hakan ya samu ne sakamakon hadin gwiwa na wani kamfanin sadarwa a Najeriya mai suna Smile Communication wanda ke zama kamfanin samar da yanar gizo a Najeriya.

Motocin kamfanin Metro Taxi na dauke ne da wasu barobaron rubuto da ke nuni da cewar suna dauke da yanar gizo kyauta wato Free Wifi.

Priscilla Ibe Babbar ita ke lura da harkokin zirga-zirgar motocin haya masu dauke da yanar gizo a birnin Legas, ta bayyana cewar kamfanin yana samar yanar gizo ne kyauta ga motocinsu ta yadda fasinjoji za su amfana duk lokacin da suka fuskanci matsanancin cinkoso a kan hanyoyin mota a birnin.

Still DW Beitrag Internetzugang in Metro Taxi Lagos
Hoto: DW

"Ka san idan kana da abokin hulda wanda cunkosan hanya ya tsare shi kimanin wasu awanni kuma kana da wasu rahotanni da kake son dubawa, kuma kana da Email din ka da za ka duba a maimakon ka tsaya kana bata lokacinka a banza, kana da yanar gizo da za ta dauke maka kewa, shi ke nan sai ka fara shawagin ka a yanar gizon. Ga dalibai muna da dandalin sada zumunta domin sanin yadda duniya take. Kana kuma da damar da za ka samu rahotanni yadda cunkoso zai dunga wakana a wasu sassan birnin, kana kuma da damar samun labarai a yayin da ake tafiya"

Charles Offiah wani kwarrare ne a harkokin sadarwa ya yi karin haske kan irin yadda harkokin yanar gizon kyauta suka sauya tunanin mutane.

"Harkar yanar gizo tana debe min kewa tana sanya ni himmatuwa kan wasu al'amura. Ina saduwa da abokan hulda ta. Tun da ko da yaushe ina halartar tarurruka, hakan yana bani damar saduwa da kowa. Abu ne mai sauki idan aka yi la'akari da yadda kake kan hanya. Yanar gizo za ta sada ka da abokan huldarka."

Tuki a tsanake ba damuwa daga fasinja

Ebola in Lagos – Zwischen Panik und Normalität
Cinkoson ababen hawa ba sabon abu ba ne a LegasHoto: DW/A. Kriesch

Janyo hankulan fasinjoji na mai nuni da cewar harka ta fara kankama ga direbobin motocin haya a Legas. Segun Bamgbose ya ce yanzu haka irin damuwar da fasinjoji suke samu lokacin cinkoson ababen hawa ta kau sabili da yanar gizo kyauta.

"Lallai an samu raguwar damuwar, babu komai yanzu ta fusakar cewar kai maza-maza musamman idan fasinja yana sauri a lokacin da direba ya gigice. To amma yanzu fasinjoji suna cikin kwanciyar hankali."

Harkokin zirga zirgar ababen hawa na haya da ke tattare da yanar gizo wani tsari ne da aka bullo da shi mai kyau domin saukaka wahalhalun fasinjoji lokacin cinkoson ababen hawa. Mai yiwuwa ne ma a samu wasu mutane da ke son a kara tsagaitawa domin su more harkokin yanar gigon kyauta a Nijeriya.