Hadin-gwiwa tsakanin bankunan Tarayyar Turai(EU) | Labarai | DW | 19.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hadin-gwiwa tsakanin bankunan Tarayyar Turai(EU)

Shugabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai(EU) sun daideta kan kafa wani komiti na binciken aikin bankuna somi da shekara mai zuwa

A taron da suka gudanar a birnin Brussels na kasar Beljiyam shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun daideta kan kafa wani komiti na binciken aikin bankuna somi da shekara mai zuwa. Kakakin hukumar zartarwar kungiyar ya ce a dangane da haka akwai bukatar cimma wata matsaya ta siyasa domin tabbatar da aikin hadin-gwiwa tsakanin bankuna muddin ana bukatar fara aiki da wannan tsari a shekarar 2013. Wani jami'in kasar Faransa ya ce wannan komitin zai hada ne da dukkan ma'aikatun kudi 6000 na kasashe masu amfani da kudin Euro.

Da farko an samu sabanin ra'ayi tsakanin Jamus da Faransa bisa kafa wannan komiti. A lokaci da a hannun daya gwamnatin Jamus ta nuna rashin amincewa da fara aikin komitin daga ranar daya ga watan Janairu, gwamnatin Faransa a dayan hannun kira ta yi da a soma aiki da shi a farkon shekara mai zuwa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu