Gwamnoni na musanta zargin boye kayayyakin tallafin abinci | BATUTUWA | DW | 26.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Gwamnoni na musanta zargin boye kayayyakin tallafin abinci

A yayin da ake ci gaba da wasoso a rumbunan ajiyan kayan abinci a jihohi dabam-dabam cikin tarrayar Najeriya, kungiyar gwamnonin kasar ta musanta boye kayayyakin tallafin da aka samar na annobar corona.

Kama daga yankin arewacin Najeriya ya zuwa yankin kudu ake ci gaba da farfasa rumbunan ajiya na gwamnatoci na jihohi dama na masu kasuwa da sunan wasoson kayan masarufi a jihohi  dabam-dabam. A Abuja dai wasoson ya ci gaba har ya zuwa wannan Litinin a garin Gwagwalada inda wasu matasa suka farma rumbunan ajiyar kayayyakin suka wawashe kayan amfanin gona.

Duk da cewar dai sannu a hankali al'adar wasoson na dada bazuwa ya zuwa jihohin arewacin kasar, daga dukkan alamu abun da ke faruwar ba shi ruwa da tsaki da batun yunwar da ake ta'allakawa da karuwar tashi na hankalin. Can a jihar Yobe da ke zama daya a cikin jihohin da ko bayan Covid-19, suke kuma fuskantar tashin hankali na ta'addanci.

Nigeria Lagos | Protest EndSARS

Zanga-zangar ENDSARS ce ta rikide zuwa rikici da wasoson kayayyakin abinci

An dai share wunin wannan rana ana wani taron gaggawa na majalisar tattalin arziki  ta gwamnoni na kasar, bayan zargin boye kayan na tallafi a bangare na gwamnonin kasar da ke da mallaki na rumbunan ajiyar. Amma a cewar Abdurazak Bello Barkindo da ke zaman kakaki na kungiyar gwamnoni ta kasar, akwai  rashin na fahimta ga masu zargin gwamnonin da boye kaya a cikin tsakiyar hali na bukata.

To sai dai kuma akwai fargabar yiwuwa a ci guba a tsakani na dubbai na matasan da suka wasashe abubuwa dabam-dabam, kama daga shi kansa abincin ya zuwa ga irin shuka, dama sinadarai da sunan korar yunwar.Tarrayar Najeriyar dai na a tsakanin dadadawa matasan da ke ci gaba a cikin karatun rikici da kuma fuskantar makoma mara tabbas sakamakon rikidewar bukatun ya zuwa wasoso na dukiyar al'umma.

 

Sauti da bidiyo akan labarin