Gwamnatin Najeriya ta ce mutum daya ya yi saura me cutar Ebola | Labarai | DW | 26.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Najeriya ta ce mutum daya ya yi saura me cutar Ebola

Da alamu dai gwamnatin Najeriya na ci gaba da samun nasara a yakin da ta ke yi da cutar Ebola,bayan da gwamnati ta sake bayyana sallamar wasu mutane da suka warke.

Mahukunta a Abuja fadar gwamnatin Najeriya sun bayyana a ranar Talatannan cewa an sake sallamar wasu karin mutane biyu daga cibiyar da aka killace su, sakamakon harbuwa da kwayoyin cutar Ebola mai saurin hallaka mutane. Wannan ya sanya saura mutum daya a wannan cibiya da aka killace wanda ke dauke da wannan cuta.

Kamar yadda wata kididdiga ta maaikatar lafiya ta fitar, Najeriya ta samu mutane 13 wadanda aka tabbatar da sun kamu da cutar ciki kuwa har da Patrick Sawyer, wanda shi ya kai cutar birnin Legas da ke a kudu maso yammacin Najeriya, ya kuma ce ga garin ku nan a ranar 20 ga watan Yuli na wannan shekara.

Gaba daya dai mutane biyar ne suka mutu ta sanadiyar kamuwa da kwayoyin cutar a Najeriya.

Ministan lafiya Onyebuchi Chukwu ya bayyana cewa sallamar wadannan marasa lafiya da suka warke guda 2, ya sanya adadin wadanda aka sallama suka kai mutane 7.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdourrahmane Hassane