1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Gwamnan Kano ya fita daga NNPP

Lateefa Mustapha Ja'afar SB
January 23, 2026

Gwamnan jihar Kano a Tarayyar Najeriya Injiniya Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da ficewarsa daga jammiyyar NNPP, bayan tsahon lokaci ana jiran tsammani.

https://p.dw.com/p/57LwY
Gwamna Abba Kabir Yusuf  na jihar Kano da ke Najeriya
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ke NajeriyaHoto: Nasiru Salisu Zango

Da yammmacin Jumma'ar 23 ga watan Janairun 2026 ne, wata tawaga karkashin mai maagana da yawun gwamnan na Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ta ziyarci mazabar Diso a karamar hukumar Gwale, inda nan ne mazabar gwamna Abba tare da mika takardar da ke kunshe da sakon gwamnan na ficewa daga jamiyyar. Wakilinmu a Kanon Nasir Salisu Zango ya ruwaito mai magana da yawun gwamnan na mai bayyana cewa, ficewar gwamnan tare da 'yan majalisun tarayya takwas da na jiha 20 da kuma shugabannin kananan hukumomi 44, ta biyo bayan rikici da ya dabaibaye NNPP din.