Gwamman mutane ne suka halaka a Yemen | Labarai | DW | 19.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamman mutane ne suka halaka a Yemen

A na dai kokari na kawo karshen zubar da jini a wannan kasa tun bayan shigar Saudiyya a watan Maris na shekarar 2015 dan tallafa wa gwamnatin Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi.

Rikici da ya barke a tsakanin mayaka a Yemen gabannin tattaunawar zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke shiga tsakani a wannan Laraba ya yi sanadi na kisan gwamman mayakan da ke shan matsin lamba na su rungumi matakan zaman lafiya dan kawo karshen shekaru biyu na yakin basasar da kasar ta fada.

Shirin yarjejeniyar dai na zama karo na shida a kokari na kawo karshen zubar da jini a wannan kasa tun bayan shigar Saudiyya a watan Maris na shekarar 2015 dan tallafa wa gwamnatin Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi bayan da 'yan tawayen suka mamayi yankuna da dama na Yemen.

Fararen hula dai da dama sun halaka a yakin da wannan kasa ta Yemen ta fada wanda ya lakume rayukan mutane 6,900 sama da rabin adadin da ke zama fararen hula.