Takarar zaben Najeriya 2019
February 21, 2019Talla
Hukumar zabe ta kasa INEC ta ce shirya tsaf domin gudanar da zabe a wannan asabar din 23 ga watan Fabrairu 2019.
A makon da ya gabata ne dai hukumar ta INEC ta dage zaben bisa dalilai na matsalar rashin isar kayan zabe a wasu yankunan kasar.
Shugaban kasar Muhammadu BUhari da ke neman wa'adi na biyu da kuma babban mai kalubalantarsa Atiku Abubakar kowannensu ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar mafi girma a Afirka.