Guterres ya yaba shari′ar ′yan Boko Haram a Najeriya | Duka rahotanni | DW | 09.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Guterres ya yaba shari'ar 'yan Boko Haram a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa Najeriya kan yadda ake shari'ar mayakan Boko Haram da ake tsare da su da kuma yadda ake kare hakkin bil Adama

Den Haag Schlusszeremonie des UN-Kriegsverbrechertribunals für Ex-Jugoslawien | UN-GeneralSekretär Antonio Guterres (Reuters/United Photos/T. Kluiters)

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteres

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres wanda ya sanar da wannan yabo a wani rahoto da majalisar ta fitar kan ayyukanta a kasashen Afirka ta yamma ya nemi gwamnati da ma'aikatar shari'a da jami'an tsaro su tashi tsayin daka wajen ganin ana bin dokoki da yarjeniyoyi na kasa da kasa da suka shafi kare hakkin bil Adama.


Nigeria Militär Präsident Muhammadu Buhari (NPR)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da manyan jami'an soji

A zangon karshe na shekarar 2017 ne dai gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wasu mutane 1600 da ake zargi mayakan Boko Haram ne a wata shari'a da aka yi a asirce a wasu cibiyoyin tsaro inda aka yanke wa da dama daga cikinsu hukunci bayan samun su da laifi. Haka kuma yayin da shekarar ke karewa rundunar sojin Najeriya ta yanke wa wasu sojojin hukunci saboda samun su da laifin keta hakkin bani Adama matakin da ake gani ya gyara irin kallon da a baya ake yiwa Sojojin na cin zarafin jama‘a ba tare da fuskantar shari'a ba.


Sai dai wasu masu kare hakkin bil Adama kamar Barista Atiku Isma'il wani mai rajin kare hakkin dan Adama a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya na ganin majalisar ta yi gaggawarar yabo. Amma ga masu fashin baki kan harkokin yau da kullum, matakai da ake dauka na yi wa wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne Shari'a abin a yaba ne kasancewar a baya ba a samu hakan ba.

Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram (Getty Images/AFP)

Babban hafsan sojin Najeriya da kwamandan rundunar yaki da Boko Haram

Wannan yabo da Majaliar Dinkin Duniya ta yi wa mahukuntan Najeriyar dai na zuwa a dai-dai lokacin ake shirin gurfanar da wasu sabbin wadanda ake tuhuma da kasancewa 'yan Boko Haram da kuma ci gaba da shari'ar wadanda ba kammala shari'ar su ba a baya.


Jami'in Shari'a na rundunar matasan Civilian JTF Barista Jibril Gunda ya tabbatar da cewa gwamnati ta tanadi isassun lauyoyi da za su bada kariya ga duk wani dan Boko Haram da bai samu lauyan da zai kare shi a shari'ar ba.


 

 

Sauti da bidiyo akan labarin