Guterres ya caccaki shugabar Myanmar | Labarai | DW | 14.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guterres ya caccaki shugabar Myanmar

Sakatare janar na MDD António Guterres ya yi kakkausar suka ga shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi kan yadda rashin tsaro ke ci gaba da tilastwa musulman Rohingya tserewa matsugunansu.

A yayin ganawar shugabannin biyu a taron kolin kasashen kudu maso gabashin Asiya a birnin Manila, babban Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya ce wajibi shugabar ta sauya salon shugabanci da zai inganta matakan tsaro a kasar, wanda zai ba da damar maido da miliyoyin 'yan kasar da ke gudun hijira a kasar Bangaledesh.

"Ba zan iya boye radadin da nake ji kan 'yan Myanmar sama da dubu 600,000 ke galabaita a yayin gudun neman tsira ba."MDD ta ce Myanmar ta gaza kare al'ummarta

Guteres ya bukaci samar da hukumar da zai sa ido kan cin zarafin fararen hula, tare da taimakawa ayyukan jinkai a gabashin jihar Rakhine. Sakatare janar din ya kuma bukaci a maido da doka da oda zai kare hakkin kowa da kowa da zai ba da damar ci gaba da cudanya a tsakanin dukkanin kabilu da ke gaba da juna a a gabashin jihar.

Wannan matsin lamba da shugaba Aung San Suu Kyi ke fuskanta daga MDD, na zuwane kwana guda bayan wani binciken cikin gida ya wanke Sojojin kasar daga zargin aikata fyade da kisan gilla, hada cin zarfi da lalata dukiyar muslman Rohingya da ke jihar Rakhine.Aung San Suu Kyi ta ziyarci jihar Rakhine a MyanmarJirgin ruwa ya kife da 'yan Rohingya

DW.COM