Aung San Suu Kyi ta ziyarci jihar Rakhine a Myanmar | Labarai | DW | 02.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aung San Suu Kyi ta ziyarci jihar Rakhine a Myanmar

Ana dai zargin jami'an tsaro na Myanmar da aikata fyade da kona gidaje da ma kisa na al'umma a jihar ta Rakhine da 'yan Rohingya Musulmi ke da rinjaye. saboda haka ne Suu Kyi ta kai ziyara.

Jagorar al'umma a Myanmar Aung San Suu Kyi  a wannan rana ta Alhamis ta kai ziyara jihar Rakhine me fama da rikici inda sama mutane dubu dari biyar suka kaurace wa jihar saboda gallabar jami'an tsaro. Aung San Suu Kyi me fada a ji a wannan kasa ta Myanmar na ci gaba da shan suka ta kasa da kasa saboda gazawarta wajen sukar ayyukan jami'an tsaro da ake zargi da aikata fyade da kona gidaje da ma kisan al'umma tun bayan da rikici ya barke a jihar a watan Agusta da ya gabata.

Mai magana da yawun gwamnatin Myanmar Zaw Htay ya fada wa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewa  Aung San Suu Kyi ta tsara ziyarar birnin Sittwe babban birnin jihar ta Rakhine da ma wani bangare na Arewacin jihar a ziyarar ta kwana guda.

Fiye da al'ummar Rohingya 600,000 ne dai suka tsallake jihar ta Rakhine a Myanmar inda suka nemi mafaka a wasu sansanoni marasa kyau a Bangaladash. A cewar kungiyar agaji ta Save the Children, yaro daya cikin hudu  cikin wannan al'umma na fama da matsala ta rashin abinci mai gina jiki.