Aung San Suu Kyi 'yar siyasa ce ta jam'iyyar National League for Democracy (NLD). Suu Kyi ta jima a tsare saboda fafutukarta wajen ganin an girka dimokradiyya kasar.
Suu Kyi ta sha gwagwarmaya da sojojin kasar lokacin da suke mulki kafin daga bisani a sallameta daga gidan kaso har ma ta shiga harkoki na siyasa. Fafutukarta ta sanya ta samun lambar yabo ta Nobel.