Myanmar ta amince a sa ido kan zabenta | Labarai | DW | 24.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Myanmar ta amince a sa ido kan zabenta

Gwamnatin Myanmar ta ce za ta gayyaci masu sanya idanu na kasashen ketare don zuwa kasar da nufin sanya idanu kan zabe da za ayi nan gaba a wannan shekarar.

Guda daga cikin ministocin kasar Soe Thein ya ce za su gayyaci masu sanya idon ne daga kungiyar tarayyar Turai ta EU da kuma Amirka don duba yadda zaben zai gudana kuma gwamnati ba za ta yi musu katsalanda ba wajen aikinsu.

Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 65 da suka gabata masu sanya idanu daga kasashen yamma za su je Myanmar din domin sanya idanu kan yadda zabukan kasar za su wakana.