Makomar fursunonin siyasa a Burma | Labarai | DW | 23.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makomar fursunonin siyasa a Burma

Gwamnatin Burma ta bayyana kudirin sakin fursunonin siyasa 70.

Hukumomin Burma ko kuma Myammar, sun amince da sakin fursunonin siyasa 70 a wannan Talatar (23. 07. 13), bayan da shugaban kasar Thein Sin ya sha alwashin sallamar daukacin wadanda ke tsare nan da karshen wannan shekarar. Wannan matakin, da ke zama na baya bayan nan a jerin sauye-sauyen da shugaban kasar, wanda ke zama tsohon janar na soji ke samar wa dai, kungiyoyin fararen hula na dari-darin nuna farin cikinsu da shi, domin kuwa a cewarsu - ha yanzu gwamnati na tsare masu adawa da ita.

Hla Maung Shwe, da ke zama babban mai bada shawara ga shugaban kasar Burma, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, tuni shugaban ya sanya hannu a kan dokar yin afuwa ga fursunoni 70 din.

Dama a lokacin wata ziyarar aikin da ya kai birnin London na Birtaniya a makon jiya ne, shugaba Thein Sein na Burma ya yi alkawarin sakin daukacin fursunonin siyasar sannu a hankali. Ya dai kai ziyarar ce, a ci gaba da rangadin kasashen Turai da yake yi a kokarin sake mayar da martabar kasarsa, bayan saniyar waren da ta fuskanta sakamakon gallaza mwa jagorar adawar kasar Aug San Suu Kyi a shekarun baya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman