Myanmar: Bincike kan kisan kiyashi | Labarai | DW | 06.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Myanmar: Bincike kan kisan kiyashi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta gudanar da bincike kan rikicin da ke cigaba da ruruwa a wasu sassan kasar Myanmar ko Burma ciki kuwa har da kisan da ake yi wa musulmin kasar 'yan kabilar Rohingya.

Yanghee Lee da Majalisar Dinkin Duniya ta aike kasar ta Burma a matsayin wakiliya ta musamman kan kare hakkin dan Adam ta ce za a fara wannan bincike ne cikin makon gobe idan ta kai ziyara kasar musamman jihar Kacin inda rikicin kabilaci tsakanin 'yan tawaye da sojoji ya yi sanadin rasuwar mutane da dama. Gabannin wannan ziyara da za ta kai, Lee ta yi kakkausar suka ga hukumomin kasar sakamakon abinda ta kira nuna halin ko in kula da abinda ke faruwa a jihar Rakhine inda 'yan kabilar Rohingya ke zaune, lamarin da ya sanya da dama daga cikinsu yin hijira zuwa wasu bangarori na Bangladesh. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama da dama sun yi ta nuna damuwa kan irin halin da Musulmi 'yan kabilar Rohingya ke ciki a kasar ta Burma inda suka yi ta yin kiraye-kiraye na a duba halin da suke ciki don kawo karshen kisan da ake musu ba gaira ba dalili.