Jirgin ruwa ya kife da ′yan Rohingya | Labarai | DW | 09.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin ruwa ya kife da 'yan Rohingya

Mutane 12 sun mutu yayin da jirgin ruwa makare da Musulman Rohingya da ke tserewa zuwa Bangledesh ya nitse a ruwa. Hukumomin kula da gabar ruwan sun ce cikin gawarwakin akwai kananan yara guda biyar.

Rahotanin 'yan sanda na cewa cikin mutane 35 da ke cunkushe a cikin kwale-kwalen, mutane takwas kadai suka tsira da kyar. To sai dai masu ayyukan ceto a ruwan sun ce babu tabbacin adadin mutanen da suka bata a cikin ruwan kawo yanzu.

Tun bayan barkewar rikicin kabilanci a yankin na Rohingya a watan Agusta, dubban 'yan yankin ke gudun hijira a makociyar kasar wato Bangledesh. Kamarin rikicin ne dai ya sa gwamnatin Bangledesh jaddada matakan tana ci gaba da ba wa 'yan Rohingyan mafaka da kayan agaji. Amma sun gargadi gwamnatin kasar Myanmar da su dau matakan gaggawa da zai kawo karshen rikicin don a samu a maido da 'yan gudun hijiran kasar da ke galabaita.