Guinea na shirin ban kwana da Ebola | Labarai | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guinea na shirin ban kwana da Ebola

Mahukuntan Guinea sun bayyana nasara kan cutar Ebola bayan an sallami mara lafiya na karshe da cutar daga asibiti.

Mahukuntan kasar Guinea Conakry sun tabbatar da cewa mara lafiya na karshe dauke da cutar Ebola ta samu sauki. Yarinyar 'yar shekaru biya da haihuwa da ke karkashin kulawa an sallame ta daga asibiti a wannan Talata, abin da ke nuna shiga matakin kirga kwanaki 42, bisa tsarin hukumar lafiya ta duniya, idan babu wanda ya sake kamuwa da cutar sai a fitar da kasar daga cikin wadda take karkashin annobar cutar ta Ebola.

Cutar Ebola ta yi sanadiyar hallaka fiye da mutane dubu-11 galibi a kasashen yankin yammacin Afirka, amma da taimakon kasashen duniya aka dakile cutar. A farkon wannan wata na Nuwamba kasar Saliyo ta samu nasarar ficewa daga cikin masu dauke da cutar, tun farko Laberiya ta samu irin wannan nasara.