Guido Westerwelle-Kwarewa a cikin aiki? | Jigo | DW | 04.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Jigo

Guido Westerwelle-Kwarewa a cikin aiki?

Guguwar sauyi a kasashen Larabawa da rikici a Turai: wannan aiki ne mai wuya ga wani ministan harkokin waje, sabon shiga da kuma ke aiki da wata shugabar gwamnati da ta kware.

Ga Guido Westerwelle sauyi daga kujerar 'yan adawa ya zuwa mukami mafi girma a ma'aikatar harkokin waje, babbar nasara ce. Gabanin haka Westerwelle da ya kasance shugaban FDP ya jagoranci jam'iyyarsa a zaben 2009 inda ta ba da mamaki na yawan kuri'u kimanin kashi 15 cikin 100 da ta samu. Hakan ya kai sa ga kololuwar aikinsa wato ministan harkokin waje kuma mataimakin shugabar gwamnati. Sai dai da farko sabon ministan harkokin wajen, Westerwell ya yi ta katsalanda a harkokin cikin gida ba tare da ya mayar da hankali sosai a kan ma'aikatar harkokin wajen ba.

Bayan matsin lamba da ya sha a farkon watan Afrilun shekarar 2011 ya sauka daga kan mukamin shugaban jam'iyyar FDP da na mataimakin shugabar gwamnati. Wannan mataki da ya dauka ya ba shi damar mayar da hankali kacokan a kan aikinsa na babban jami'in diplomasiyar Jamus, inda ya kuma samu nasarar tafiyar da aikinsa, inji Ruprecht Polenz shugaban kwamitin harkokin waje kuma dan jam'iyyar CDU.

"Ina jin kowa ya ga yadda yake tafiyar da aikinsa na ministan harkokin waje cikin so da kauna. Yana duba batutuwa da idanun basira kana yana kokarin kare bukatun Jamus a cikin nahiyar Turai dake kara hadewa wuri daya tana kuma bunkasa. Yana burge ni domin ba ya yin gaban kansa, yana la'akari da sauran kasashen Turai."

Shugabar gwamnati mai angizo da minista mai rauni?

German Chancellor Angela Merkel arrives for the weekly cabinet meeting at the chancellery in Berlin, Germany, Wednesday, Oct. 17, 2012. (Foto:Michael Sohn/AP/dapd)

Merkel ta yi wa manufofin ketare kane-kane

Shi ma Gunther Hellmann masanin kimiyyar siyasa na da irin wannan ra'ayi cewa Westerwelle ya zama wani ministan harkokin waje da ya nuna sanin makamar aiki ko da yake da akwai dan nakasu a gareshi.

"Sai dai Westerwelle ba ministan harkokin waje ne mai kwari ba. Da wuya ga wani ministan harkokin waje ya samu gagarumin yabo idan yana aiki ne da wata shugabar gwamnati wadda ta rigaya ta kware kuma ta saba da aiki, kuma a tsanake tana mayar da martani a lokacin da ya kamata."

Ga misali an mayar da yawa daga cikin batutuwan da suka shafi yarjejeniyar Lissbon ta shekarar 2007 karkashin ofishin shugabar gwamnati sannan Merkel ta yi amfani da ikonta ta mayar da kadan na shawarwarin manufofin ketare marasa dadi ga ministan harkokin wajen. Hakan ya fito fili lokacin zartas da kuduri kan rikicin Libiya a Kwamitin Sulhu a cikin watan Maris na shekarar 2011, inda Westerwelle ya yi rowar kuri'arsa lokacin kada kuri'ar haramta shawagin jiragen sama a yakin basasan Libiya. Westerwelle ya sha suka daga 'yan adawa da ma wasu kafafan yada labarai dangane da wannan mataki, duk da cewa a hakika Merkel da ministan tsaro Thomas de Maiziere sun taka rawa wajen daukar wannan mataki.

Sukar lamirin Westerwelle

Shi kuwa a nasa bangaren masanin harkokin waje na jam'iyyar SPD Rolf Mützenich cewa ya yi a cikin shekaru hudun nan Westerwelle ya zama tamkar dan amshin shata ne, kuma a karshen wannan wa'adin mulki bai san inda ma ministan ya dosa ba.

Der außenpolitische Experte der SPD-Fraktion Dr. Rolf Mützenich im Gespräch mit DW-TV am 14.6.2013 in Berlin.

Dan jam'iyyar SPD Rolf Mützenich

Ya soki ministan da ayyana wasu kasashe kamar China da Kasachstan da kuma Malaysia dake fatali da hakkin dan Adam da tsarin demokradiyya a matsayin kawaye da ke da ikon fada a ji kuma ke da muhimmanci ga Jamus.

"Wannan batun tamkar sanya wata alkibla ce da irin kasashen da za mu yi cinikin makamai da su, domin akwai irin su Saudiyya da Indonesiya da kuma Qatar, saboda haka tambayar da nake ita ce wai me wata ma'amala za mu yi da waddannan kasashe da a karshe za ta dace da bukatunmu da kuma manufofinmu?"

Dan SPD ya ce Westerwelle ya yi alkawarin rage makaman nukiliya, amma maimakon ya mayar da hankali wajen cika wannan alkawari, tarayyar Jamus ta zama wata kasa da ke kara tura makamai zuwa yankunan da ake fama da rigingimu kamar yankin tsibirin kasashen Larabawa.

Matakin tura wa gwamnatin Saudiyya da makamai wani ra'ayi ne na Merkel da ke cewa maimakon Jamus ta tura sojoji don rage radadin rikice-rikice a yankuna masu fama da tashe-tashen hankula to kamata ya yi ta tura wa kasashe masu karfi a wadannan yankuna da makamai.

Mawallafa: Bettina Marx / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourrahmane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin