1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta kashe mutane a Najeriya

June 29, 2018

Hukumomi a Najeriya sun ce mutane sun mutu a birnin Legas, lokacin da wata tankar mai ta fadi ta kuma kone kurmus.

https://p.dw.com/p/30WBh
Nigeria Explosion Pipeline
Hoto: picture-alliance/ dpa

Jami'ai a Najeriya sun ce mutane tara ne suka mutu a birnin Legas da ke yankin kudu maso yammacin kasar, lokacin da wata tankar mai ta fadi ta kuma kone kurmus a kan wata gadar da ke a birnin.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta ce daga cikin wadanda suka mutun har da wani yaro karami, to sai dai wadanda suka shaida lamarin sun ce yawan wanda suka mutun zai iya zarta haka.

Akwai kuma wasu mutum hudu da suka sami munanan kuna a lamarin da ya auku da yammacin ranar Alhamis.

Haka ma wasu motoci 54 sun kone kurmus a lamarin da ba a kai ga tantance abin da ya haddasa faduwar da motar ta yi ba.

Birnin Legas dai shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirka, da kuma ke dauke ke da mutane miliyan 21.