Girka ta ki bude kofa ga ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 28.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka ta ki bude kofa ga 'yan gudun hijira

Rahotanni daga Girka na cewa mahukumta sun ce ba za su bar 'yan gudun hijira su shigo ba tare da izini ba, Kuma za su kara tsaurara sintiri na musamman a iyakokinsu domin ganin babu wani dan gudun hijira da ya shigo.

Rahotanni suka ce akwai 'yan gudun hijira 300 ciki har da mata da kananan yara da ke kan hanyarsu ta zuwa Girka bayan sun kaurace wa muhallinsu a yankin Idlib na Siriya. Amma Firaministan kasar Girka Kyriakos Mitsotakis ya ce ba za ta sabu ba.

Yan gudun hijira dai sun fara taruruwa a kan iyakar Girka da ke kusa da kasar Turkiyya ne bayan da suka sami labarin cewa Turkiyya ta yi barazanar bude iyakarta ga masu son zuwa nahiyar Turai.

To amma Firaministan ya ce kasar Girka ba ta da hannu a cikin rikicin Siriya, a don haka bai kamata a kawo mata wata dawainiya ta 'yan gudun hijira ba,