Girka da Rasha na neman karfafa hulda | Siyasa | DW | 08.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Girka da Rasha na neman karfafa hulda

Firaministan Girka Alexis Tsipras na ziyarar aiki a kasar Rasha, Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da Girka mai fama da matsalolin bashi, ke neman kudi ruwa a jallo

Alexis Tsipras ya yi amannar cewa takunkuman kasashen yamma a kan Rasha, sun kuma shafi kamfanonin Girka. Saboda haka ne ma batun takunkuman ya zama daya daga cikin muhamman batutuwan da tattaunawar tsakanin shi da shugaban Rasha Vladimir Putin. Sai dai Girka ba za ta iya kai wa ga cire wa Rasha takunkuman ba, inji Michail Krutichin na kamfanin makamashin RusEnergy. Ya ce Girka ba ta da niyyar fita daga kungiyar EU, ba za ta kuma nuna tana da kawaye bayan EU ba, amma dole ne ta nuna cewa tana tare da EU.

Sai dai a wata hira da DW, Michail Kassajnow tsohon Firaministan Rasha kuma daya daga cikin shugabannin jam'iyyar adawa ta RPR-PARNAS ya ce wannan kawai shi ne bukatar fadar Kremlin, kasancewa Girka ba ta amince da wasu manufofin EU ba, kuma wannan tamkar raba kan tarayyar Turai ne.Ya ce: "Putin da kansa ya mayar da kansa saniyar ware a cikin gamayyar kasa da kasa. Burinsa a nan guda daya ne, wato lalata dangantaka tsakanin kasashen Turai kansu da kuma tsakaninsu da kasar Amirka. Putin so yake EU ta rushe, yadda Amirka kadai za ta zama abokiyar gabarsa."

Mahukuntan Rasha na da karin dalilin neman kusanci da Girka, inji Michail Krutichin na kamfanin RusEnergy.

Ya ce: "Rasha na da karancin abokan hulda da kuma rashin shugabanni da za su zauna teburi guda da hukumomin Mosko. Idan Rasha ta gamsu wasu kawaye irinsu su janhuriyoyin Nauru da Vanuatu, hakan zai kasance tamkar wani mafarkin samun wata kasa a Turai da ke da shirin mika wa shugabannin Rasha hannu."

Masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin cewa, Mosko na kokarin samun amincewar daidaikun kasashen Turai, ta hanyar ba su basussuka. Ba Girka kadai ba, har da irinsu Hungary wadda kwanakin bayan Rasha ta ba ta rancen Euro miliyan dubu 10, da Cyprus wadda a shekarar 2011 ta samu Euro miliyan dubu 2.5 daga Mosko. Sai dai babu tabbas ko Girka da Rasha za su amince da wata yarjejeniyar tallafin kudi.Duk da haka fatan Firaministan na Girka Alexis Tsipras shi ne tattaunawar tsakanin kasarsa da Rasha, ta yi tasiri ga shugabannin EU, inji masanin na kamfanin RusEnergy Michail Krutichin:

Ya ce: "Tattaunawa za ta nuna cewa Girka na da kawaye kuma za ta iya kaiwa gaci, ba tare da wani tallafi daga tarayyar Turai ba. Akwai alamun cewa sassan biyu na son yin wata burga ce a siyasance."

Wasu masanan kuma na da ra'ayin cewa kasar Girka ba za ta iya neman taimakon kudi daga Rasha ba, matukar ba ta 'yantar da kanta daga hukumomin kudi na EU ba.

Wani batun da shugabannin biyu za su kuma duba shi ne iskar gas, inda ake sa rai Rasha za ta yi wa Girka wani rangomen farashin na iskar gas, ta kuma rage yawan makamashin da ta ke tura wa Girka kamar yadda hukumomin a Athens suka nema tun a bara. A nasu bangaren Kasashen EU dai na zargin Putin da kokarin raba kan kasashen kungiyar.

Sauti da bidiyo akan labarin