1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana tana tattaunawa da Najeriya don warware takaddamar gas

Mohammad Nasiru AwalOctober 15, 2015

Kamfanin man fetir na Najeriya NNPC ya yi barazanar katse tura gas zuwa Ghana saboda bashin da yake bin kasar da ya kia dalar Amirka miliyan 181.

https://p.dw.com/p/1Gp4v
Ghana Präsident John Dramani Mahama
Shugaban Ghana John Dramani MahamaHoto: BDI/C. Kruppa

Wata tawagar gwamnatin kasar Ghana na wata tattaunawa ta gaggauwa a Najeriya da nufin hana aiwatar da barazanar katse tura mata da iskar gas daga Najeriya. Wani kakakin gwamnatin Ghana ya nunar da cewa tun a daren ranar Laraba tawagar ta tashi zuwa Najeriya inda ya yi fatan za ta shawo kan lamarin don hana fadawa cikin wani rikicin makamashin gas a kasar ta Ghana. Da farko kamfanin man fetir ta kasa a Najeriya wato NNPC ya ce zai rage yawan gas da yake tura wa tashar samar da wutar lantarki ta Ghana da kashi 70 cikin 100 a wannan Jumma'a, saboda rashin biyansa bashin dalar Amirka miliyan 181 da yake bin kasar ta Ghana. Da ma dai Ghana na fama da yawan daukewar wutar lantarki kuma gas daga Najeriya na samar da kashi 25 cikin 100 na makamashin da Ghanar ke bukata.