1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gaza: Amurka ta mika wa MDD daftarin tsagaita wuta

March 21, 2024

Sakataren harkokin wajen Amurka ya sanar da cewa Amurka ta gabatar da wani daftarin kudiri ga kwamitin sulhu na MDD inda ta bukaci da a tsagaita wuta a Gaza tare da sako ragowar mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/4dxVp
Indien | G20 Antony Blinken
Hoto: Olivier Douliery/AP Photo/picture alliance

Babban jami'in diflomasiyyan Amurka Antony Blinken ya sanar da hakan ne a yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillacin labaran kasar Saudiyya na Al Hadath, inda ya ce yana fatan kasashe mambobin kwamitin za su mara baya ga wannan daftari domin samar da mafita ga rikicin na Gaza da ke ci gaba da lakume rayukan fararen hula.

Karin bayani: Antony Blinken zai je Saudi Arabiya da Masar kan batun yakin Gaza

Mista Blinken dai na rangadi ne a yankin Gabas ta Tsakiya a kokarin warware rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas wanda ya shiga wata na shida, inda ya fara daga Saudiyya kuma zai yada zango a wannan Alhamis a kasar Masar kafin daga bisani ya isa birnin Doha na kasar Qatar.