Gasar kwallon Kwando na Turai | Zamantakewa | DW | 28.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gasar kwallon Kwando na Turai

Kasar Spain ta dauki kofin na wannan karon bayan ta doke Faransa da ci 71 da 55

A wasannin kwallon kwando na nahiyar Turai da aka yi a birnin Prague na Tchikoslovakiya, kasar Spain ta samu nasara a kan Faransa da ci 71 da 55, abinda ya bata damar daukar kofin da dama shekaru hudun da suka wuce kasar ce ta samu nasara a bangaran mata a shekara ta 2013.

Ita kuwa kuma kasar Beljiyam ta samu lambobin yabo na tagula bayan da suka lashe kasar Girka da ci 78 da 45,kuma wannan zai baiwa Beljiyam din damar halartar gasar duniya ta kwallon kwando a karon farko wacce za a yi a Spain a shekara ta 2018.