1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An Fitar da Ghana da Najeriya daga gasar mata

Gazali Abdou Tasawa
August 21, 2018

Ana cigaba da gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 a kasar Faransa inda kasashen Ghana da Najeriya ke wakiltar Nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/33UOu
France Soccer FIFA Womens´s World Cup
Hoto: picture-alliance/epa/Andre Pichette

Sai dai bayan da aka kori Ghana tun a zagayen farko ita ma Najeriya ta bi sahunta bayan da ta sha kashi a hannun kasar Spain da ci biyu da a wasan kwata Final. A wasan kusa da na karshe a wannan Litinin Ingila za ta kara da Japan a yayin da Faransa za ta fafata da Spain