1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bude gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

Emily Sherwin BAZ
June 14, 2018

Farin ciki da annashuwa da al'ummar Rasha ke ciki na daukar nauyin wasan ba wai a birane 11 na kasar da za a buga wasanni ya tsaya ba, har ma da sauran kauyuka da ke wajen birnin na kasar.

https://p.dw.com/p/2zaRZ
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Gambarini

Haka ma batun ya ke ta hanyar bunkasar hada-hadar kasuwanci da zuba jari da kasar ke samu. Duk da saukar ruwan sama, wannan bai hana ma'abota wasan kwallon yin dandazo a filin wasan da ke a garin Fedino domin ganin yadda za ta kaya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta garin da kuma wata kungiyar daga Moscow. Mafi akasarin al'ummar Rasha sun bayyana farin ciki da kasar ke daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniyar. Duk da cewa Fedino na da tazarar nisan kilomita 100 daga Moscow amma a hada-hadar shirye-shiryen suna ji tamkar a kasar suke.

Russland Fußball WM 2018 |  Russland vs  Saudi Arabien
Rasha ta doke takwararta ta Saudiyya da ci biyar da nemaHoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/V. Caivano

A babban birnin kasar Moscow, tuni aka gyara hanyoyin mota dana jiragen kasa, duk an yi musu sabon fainti. Tawagar masu ruwa da tsaki a harkar wasan sun kiyasta cewa an kashe sama da Euro biliyan tara a gyare-gyaren kayata kasar. Al'ummar garin Fedino na fatan ganin wannan wasan kwallon kafa zaikawo musu sauyi musammamn ma ta bangaren wasanni. Gabannin soma gasar akwai batun da a ke na sake gina wani sabon filin wasa a Voskresenk birnin da ke kusa da Fedino da zummar karbar bakuncin tawagar 'yan wasan, garin na da bukatar a samar masa da filin wasa domin kuwa guda daya tilo suke da shi, wanda aka gina tun a shekara ta 1966.