Neman nasara a gasar AFCON
January 17, 2022A kasar Kamaru ana ci gaba da wasannin neman cin kofin Afirka inda daga cikin kasashen 16 ake sa ran za su tsallaka zuwa matakin gaba a gasar AFCON; uku kacal ne suka samu tikitin ciki har da Kamaru mai masaukin baki da Najeriya da kuma Morocco da maki shida kowaccen su a wasanni. Amma sauran kasashen na jiran wasansu na uku domin sanin makomarsu.
Ga kuma yadda wasannin lig na Jamus da ake kira Bundesliga da aka kara a karshen mako ya kasance:
Wolfsburg 0 Hertha BSC 0
Union Berlin 2 Hoffenheim 1
Stuttgart 0 RB Leipzig 2
Mainz 05 1 Bochum 0
Borussia M'gladbach 1 Bayer Leverkusen 2
Bayan da aka shafe kwanaki goma ana kai kawo tsakanin shaharraren dan wasan Tennis Novak Djokovic da gwamnatin Australiya, kotu ta yanke hukuncin tasa keyar dan wasan bisa samun shi da laifin karya dokokin da suka shafe tanadin allurar rigakafin COVID-19. Kuma mai yiwuwa ma za'a dakatar da shi daga karawa a wasan Australiyan Open na tsawon shekaru uku masu zuwa. Wannan matakin dai ya dakusar da yanayin annushuwan da jama'a kan shiga a watan Janairun kowace shekara don dokin zuwan gasar na Tennis da aka fi sani da Australiyan Open.