1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garkuwa da Bajamushe a arewacin Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
April 16, 2018

A cewar mai magana da yawun 'yan sanda a jihar ta Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Magaji Musa Majia mutane biyar ne suka kai farmakin ga motar da ke dauke da Bajamushen.

https://p.dw.com/p/2w8Al
Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Tuni 'yan sanda suka shiga farautar masu garkuwan da BajamusheHoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Wasu 'yan bundiga sun yi garkuwa da wani Bajamushe da ke aiki a wani kamfanin gine-gine a arewacin Najeriya, abin da ke zuwa bayan harin da ya jaza rasa ran dan sanda guda kamar yadda jami'an suka bayyana.

A cewar mai magana da yawun 'yan sanda a jihar ta Kano Magaji Musa Majia mutane biyar ne suka kai farmakin ga motar da ke dauke da Bajamushen lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen aiki da misalin karfe bakwai da minti arba'in da biyar na safe. An dai shiga farautar wadanda suka yi garkuwa da Bajamushen kawo yanzu.