Garambawul a majalisar ministocin Nijar | Labarai | DW | 26.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garambawul a majalisar ministocin Nijar

A yayin da dambarwar siyasa ke ci gaba da ɗaukar hankali a jamhuriyar Nijar, shugaban ƙasa ya maye gurbin ministocin da suka ficce daga jami'yyun haɗakar da ke mulki.

Babban magatakardar gwamnatin jamhuriyar NijarGandu Zakara shi ne ya gabatar da sunayen sabbin ministocin da aka naɗa sakamakon wani garambawul ɗin da shugaban ƙasar Alhaji Mahamadou Issoufou ya gudanar ga sabuwar gomnatin da ya kafa ranar 13 ga wanann wata na Ogusta. A ƙarkashin garambawul ɗin an samu shigowar sabbin fuskoki guda huɗu a cikin majalissar ministocin ƙasar daga ciki har da mata ukku. Wannan garambawul ya biyo bayan ficewar jam'iyyar LUMANA daga cikin ƙawancan jam'iyyun da ke milki na MRN ranar 22 ga wannan wata. Hakan dai na tabbatar da cewa yunƙurin da ɓangarorin biyu suka yi na samun fahimtar juna ta yadda zai kai ga sake maido da jam'iyyar. Yau dai yan makonni kennan da kasar Nijar ta tsunduma cikin wani rikicin siyasa, a sanadiyyar gomnatin haɗin kan da shugaban kasar ya kafa wacce ta ƙunshi wasu ' yan addawan da suka shiga, duk da rashin amincewar uwar jam'iyyar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Abdourahmane Hassane