Gangamin adawar ficewar Birtaniya daga EU
September 9, 2017Talla
Shahararrun mawakan Birtaniya da wasu manyan 'yan siyasa sun shiga cikin gangamin na birnin London inda suka fantsama kan tituna suna tattaki har zuwa ginin majalisar kasa.
Masu gangamin da dama sun sanya riguna masu launin tutar EU yayin da wasu ke rike da tutar kungiyar, wasu kuwa na dauke da alluna da rubuce rubuce na adawa da ficewar Birtaniya daga EU.
Gangamin na ranar Asabar na zuwa ne a yayin da a ranar Litinin majalisar ke shirin kada kuri'a kan matakin kasar na ficewa baki daya daga cikin kungiyar ta EU.
Akalla mutane dubu hamsin ne suka shiga wannan gangami.