1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kawance mai dorewa a tsakanin Najeriya da Ghana

Uwais Abubakar Idris RGB
July 9, 2021

Ana sa ran ziyarar kakakin majalisar kasar Ghana a Abuja za ta taimaka wajen inganta alakar kasar da Najeriya da ke fama da takaddama a shekarun baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/3wHbK
Nigeria I Hon Femi Gbajabiamila und Hon Kingsford Alban Bagbin
Hoto: Office of the speaker/Nigerian Parliament

Shugabanin majalisun dokokin Najeriya da na kasar Ghana sun soma wani yunkuri na  kara sasanta rikicin cinikayya da ya shafi ‘yan kasuwar kasashen biyu, abin da ya sanya shugaban majalisar dokokin Ghana kawo ziyara ga takwaran aikinsa na Najeriya, inda suka kafa kungiyar kawance ta ‘yan majalisa a tsakaninsu.

Dauka mataki na dimflomasiya ta hanyar amfani da majalisar dokoki, ya sanya shugaban majalisar dokokin kasar Ghana Kingsford Alban Bagbin, yin tattaki zuwa Najeriyar a kan wannan batu da ya baiyana cewa mai muhimmancin gaske a tsakanin kasashen biyu, na sulhunta rikicin tattalin arziki da ya biyo bayan rufe shagunan ‘yan Najeriya da ma zargi na cin zarafinsu a Ghana, matakin da ya kai ga sanya Najeriyar cewa ba ta yarda ba. Karin Bayani: Dangantaka tsakanin Najeriya da Ghana na yin tsami

Nigeria I Hon Femi Gbajabiamila und Hon Kingsford Alban Bagbin
Femi Gbajabiamila da Kingsford Alban BagbinHoto: Office of the speaker/Nigerian Parliament

Sasantawa ko sulhu muhimmi ne a tsakanin kasashen biyu da suka dade suna da dangantaka mai tarihi na shekaru aru-aru. Duk da wannan, shugaban majalisat dokokin kasar ta Ghana Kingsford Alban Bagbin, ya baiyana cewa akwai fa sauran bukata bisa matakin da Najeriyar ta dauka na hana shigo da wasu kayayyaki daga kasashen waje, ciki har da na Ghana. Karin Bayani:  Rikicin 'yan kasuwa na son bata dangantakar Ghana da Najeriya

Duk da kusanci da ma danganataka tsakanin kasashen Afrika da ma yarjejeniyar cinikayya da aka rattabawa hannu ta sahale kasuwanci, bayanai daga hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da tattalin arzikin kasashen Afrika, na nuna cewa daga cikin cinikayyar da Afrika ta yi na dalla bilyan 460, dala biliyan 69 ne kadai suka yi a tsakaninsu na Afrika, duk da cewa mafi yawan abin da suke shigowa da shi daga wasu kasashe, ana samunsu a tsakanin junansu, abin da ke nuna da sauran gyara in har suna son ganin haske a tafiyar. Alamu na samun nasara a wannan fannin ya baiyana a kalaman da shugaban majalisar wakilan Najeriyar Femi Gbajabiamila ya bayyana.