1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musayar zafafan kalamai tsakanin Najeriya da Ghana

Uwais Abubakar Idris MNA
August 31, 2020

Ko kungiyar Ecowas za ta iya shiga tsakani a cece kucen diplomasiyya da ya ta so tsakanin Najeriya da Ghana masu karfin tattalin arziki a yammacin Afirka?

https://p.dw.com/p/3hpS8
Kombobild Ghanas Präsident Nana Akufo-Addo und Nigerias Präsident Muhammadu Buhari

Kurar rikici tsakanin Najeriya da kasar Ghana a kan zargi na cin zarafi da korar 'yan Najeriya sama da 700 da ke kasuwanci a Ghana ya kara daukan sabon salo biyo bayan musayar sakwanni tsakanin ministocin yada labarun kasahen biyu, abin da ya taso da batun shiga tsakani na kungiyar Ecowas a kan lamarin.

Mahukuntan Najeriya sun harzuka kuma ransu ya baci a kan abin da suka kira da cin zarafi da wulakancin da gwamnatin Ghana ta yi wa 'yan Najeriyar da ke zaune a kasarta. Alamun tabarbarewar dangantaka dai ya kara bayyana bayan harin da aka kai tare da rushe wani sashe na ofishin jakadancin Najeriyar a Ghana. Sai yanzu kuma ga wannan abin da 'yan Najeriyar suka ce sun dade suna fuskantar wannan matsala. Alamu na tura ta kai bango inda a karon farko Najeriyar ta kai ga jan layi da nuna cewa in fa Ghana ta ce mata kulle to za ta ce mata cas. Wannan canji ne daga abin da aka saba, inda Najeriyar kan yi shiru na nuna hali na yaya babba.

Ambassada Suleiman Dahiru tsohon jakadan Najeriya ne a kasashe da dama ya ce akwai dalilai na siyasa a abubuwan da ke faruwa.

 Lai Mohammed- "Najeriya ba za ta lamunta da wulakancin da Ghana ke wa 'yan kasarta mazauna Ghana ba"
Lai Mohammed- "Najeriya ba za ta lamunta da wulakancin da Ghana ke wa 'yan kasarta mazauna Ghana ba"Hoto: picture-alliance/dpa/K. Wigglesworth

Ministan yada labaru da al'adun gargajiya na Najeriya Lai Mohammed da ya aike da sako mai karfi a kan abubuwan da suka faru, sakon da takwaran aikinsa na kasar Ghana Kojo Oppong Nkrumah, ya mai da martani a matsayin amsa, tare da halatta tara ta dalla milyan daya da Ghana ta sanya wa 'yan kasuwar Najeriya su biya. Duk bayyana cewa shugaban kasar Ghana zai gana da takwaran aikinsa na Najeriya a kan batu amma lamari ne da ba a saba gani ba da ya sanya Najeriyar tunanin kungiyar Ecowas ta shiga cikin batun a cewar ministan harkokin wajenta Geoffrey Onyeama.

A bisa ka'idoji na zamantakewa da kungiyar Ecowas ta samar kowane dan asalin kasashe 15 na kungiyar zai iya zama ya yi kasuwanci a kowace kasa ba tare da tsangwama ba, abin da ya sanya ambatowa da ma jawo kungiyar a matsayin wacce za ta shiga tsakani.

Shugabannin kasashen Ecowas bayan wani taron koli da suka yi a Abuja a karshen shekarar 2017
Shugabannin kasashen Ecowas bayan wani taron koli da suka yi a Abuja a karshen shekarar 2017Hoto: Präsidentschaftsbüro Kap Verde

Amma ko Ecowas za ta iya yin wani tasiri a rikici na Najeriya da Ghana duk da kallon da ake mata na magen lami ba ki cizo ba ki yakushi? Ga Ambassada Suleiman Dahiru da karin bayani.

"A ganina Ecowas ba ta da karfin da za ta ce wa Najeriya ko Ghana su daina abin da suke yi ba. Da ba don Najeriya ba da Ecowas ta wargaje don kashi 61cikin 100 na kudaden da take kashewa Najeriya ke biya. Saboda haka Ecowas ba za ta iya tinkarar Najeriya da wata magana maras dadi."

A yayin da ake sa ido na taron da shugabannin Najeriya da Ghana za su yi domin sulhu, da alamu tura ta kai bango ga Najeriyar domin ko da an zo taro ba zai kasance irin wanda ake yi a baya ba, domin kuwa ba ta boye bacin ranta ba. Ko da yake akwai bukatar 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje su koyi darasi na bin dokokin kasar da suke zaune don kaucewa zargi irin wanda Ghana ta yi cewa wadanda ta kora suna aikata miyagun laifuffuka ne.