1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran na ci gaba da kai hare-hare a yankin Gulf

March 14, 2026

Iran na ci gaba da yin ruwan bama-bamai a kan muradun Amurka da ke kasashen yankin Gulf a daidai lokacin da yaki ke kara tsananata.

https://p.dw.com/p/5AP0T
Vereinigte Arabische Emirate Fudschaira 2026 | Brand in Ölanlage nach iranischem Drohnenangriff
Hoto: Altaf Qadri/AP Photo/picture alliance

Gajimaren hayaki ya turnike a wannan Asabar a wata babbar cibiyar man fetur ta Hadaddiyar Daular Larabawa, a wani abu da ya yi kama da sabon hari da Iran ke ci gaba da kai wa kan cibiyoyin makamashi na kasashen yankin Gulf.

Masu aiko da rahotanni sun ce hayaki mai duhu ya turnuke a yankin Fujairah mai babbar tashar jiragen ruwa na dakon mai, inda a baya hare-haren Iran suka auna wani rumbun ajiyar man fetur da kuma wata cibiyar kasuwanci.

Sai dai a cikin wata sanarwa hukumomin yanki sun ce tarkacen jirgi maras matuki da aka yi nasarar lalatawa ne suka haddasa gobara, sai dai ba su bayyana ainahin wuzrin da lamarin ya faru ba.

Jim kadan kafin aukuwar wannan lamari Iran ta yi gargadin cewa tashoshin jiragen ruwan Hadaddiyar Daular Larabawa na a matsayin halastattun wurare da za ta kai wa hari tare da kiran mutane da su san inda dare ya musu.

Indien Mumbai 2026 | Öltanker Shenlong Suezmax nach Passage der Straße von Hormus im Hafen
Hoto: Rafiq Maqbool/AP Photo/dpa/picture alliance

Iran ta bar jiragen ruwan Indiya sun ratsa mashigin Hormuz

Wasu jiragen dakon man Indiya guda biyu shake da iskar gaz sun ratsa ta mashigin Hormuz yayin da suke kan hanyar zuwa yammacin Indiya, kamar yadda ma'aikatar sufurin jiragen ruwa ta kasar ta sanar a yau Asabar.

A yayin wani taron manema labarai a New Delhi, sakataren ma'aikatar sufurin jiragen ruwa na Indiya Rajesh Kumar Sinha ya ce jiragen ruwan guda biyu shake da lodi sun ratsa mashigin Hormuz salim-alim da sanhin wannan safiya kuma a yanzu haka suna kan hanya.

Iran dai ta katse yawancin zirga-zirgar jiragen ruwa ta wannan mashigi mai matukar muhimmanci wanda kashi daya bisa biyar na man duniya ke bi ta cikin sa, a matsayin daya daga cikin martani ga harin da kawancen Amurka da Isra'ila suka kai mata a ranar 28 ga watan Fabarairu.