Gabon ta samu damar daukan nauyin gasar cin kofin Afirka | Labarai | DW | 08.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gabon ta samu damar daukan nauyin gasar cin kofin Afirka

Gabon ta samu damar daukan nauyin gasar neman cin kofin kwallon kafar kasashen Afirka na shekara ta 2017.

An zabi kasar ta Gabon ta dauki nauyin gasar neman cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka a shekara ta 2017 nan da shekaru biyu masu zuwa. Hakan ya tabbata a zaben da aka yi tsakanin mambobin kwamitin gudanarwa 14 a birnin Alkahira na kasar Masar.

Kasar ta Gabon ta samu nasarar a kan kasashen Ghana da Aljeriya wadanda suka nemi samun damar. Za a gudanar da wasan a filaye guda hudu da kasar take da su a Libreville, da Franceville, da Port Gentil da kuma Oyem. A shekara ta 2012 kasar ta Gabon da hadin gwiwan kasar Equatorial Guinea sun dauki nauyin gasar wanda kasar Zambiya ta lashe.

A wannan karo Gabon ta maye kasar Libiya wadda aka tsara za ta dauki nauyin gasar na Afirka a shekarar ta 2017, amma take ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula. Tuni aka fitar da jadawalin yadda kasashen za su kara wajen neman kai wa ga gasar neman cin kofin kwallon kafa na Afirka.