1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G7 na niyar kara wa Rasha takunkumi

Jane McintoshApril 26, 2014

Kasashe bakwai da suka fi karfin masana'antu a duniya sun sha alwashin sake ladabtar da Rasha sakamakon takun saka da ta ke ci gaba da yi da kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/1BoqD
Hoto: picture-alliance/dpa

Wasu rahotannin sun tabbatar da cewa kasar Rasha ta kece haddin kasar Ukraine wajen shawagi da jiragen saman yaki cikin kasar, yayin da sojojinta ke gudanar da rawar daji kusa da kan iyaka.

Zaman tankiya ya karu tun lokacin da 'yan aware masu goyon bayan Rasha suka yi garkuwa da masu saka ido na kungiyar tsaro da hadin kan Turan a garin Slovyansk na kasar ta Ukraine.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nemi Rasha ta yi amfani da karfin fada ajin da take da shi wajen kawo 'yan awaren kan teburin sulhu. An asa bangaren Shugaban Amirka Barack Obama ya ce za a kara kaimin takunkumi kan mahukuntan Rasha.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal balarabe