G20: Sabon tsarin bunkasa hulda tare da Afirka | Siyasa | DW | 14.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

G20: Sabon tsarin bunkasa hulda tare da Afirka

Jamus na son shigar da kyawawan manufofinta na tallafa wa tsarin bunkasa kasashen Afirka a gaban babban taron kungiyar G20, manufoyin da ake kallo a matsayin buri mai cike da tsammani.

A wannan sharin da ya rubuta, shugaban sashen Afirka na DW Claus Stäcker, ya dauko sharhin nasa ne da hanunka mai sanda wanda Shugaban kasar Gini Alpha Conde kana shugabantar kungiyar Tarayyar Afirka, inda ya fada wa shugabar gwamnatin jamus cewa, daya daga cikin shugabannin Afirka ya kira tsarin na kungiyar G20 da Afirka wanda ministan raya kasashe na Jamus Gerd Müller ya tsara, a matsayin tsarin Merkel. Ko da yake dai Merkel ta dan yi musmushi a lokacin, amma kowa yan san abin da Conde ke nufi, kuma dama ai ita kanta Merkel, a jawabinta na farko, ta fada wa shugabannin na Afirka cewa ana bukatar kowa ya furta abin da ke cikin zuciyarsa kan wannan tsari.

Sai dai maimakon a ji shugabannin na Afirka sun fito sun amarya da abin da ke zukatansu, sai kawai suka yi ta furta kalaman yabo ga tsarin na  na G20 da Afirka yayin zaman taron, inda suka ce hakan ko ba komai alamace ta yin aiki tare, musamman indan aka aiwatar da jadawalin da aka tsara, don za a iya cewa kasashen na G20 sun fara sauya matsayinsu ga Afirka. Hamshakan Afirka kamar Mo Ibrahim da Aliko Dangote, sun bayyan shirin a matsayin "Kawance mai cike da Anniya" tamkar dai su na kwatanta wasu kasashe da ke shirin shiga yaki. Mai jogarantar taron sau dama ya yi ta kwantata Merkel a matsayin mai abun al'ajabi. Alamar canji da fata na gari ya fara nan take daga wadanda suka halarci taron da ya gudana a Berlin.

Merkel - Basira da hangen nesa

Shirin wanda wasu suka kira "Tsarin Merkel", wanda kuma yana cikin ra'yin da Merkel ke da shi,  zai sauya daga batun taimakon raya kasashe wanda aka dade ana gudanarwa, kuma yanzu ta tabbata cewa baya raya kasashen. Domin tun shekara ta 1960 kasashen na Afirka an yi ta basu agajin kadade da suka kai Euro miliyan dubu 3, 556. ba tare da sun tsinanan abun kirki a tsawon wannan lokacin ba. Jarin kasashen Afirka a ma'aunin kasuwanci na duniya, ya nuna cewa daga kashi bakwai cikin dari a yanzu ya yi kasa izuwa kashi uku cikin dari. A yanzu kasashen sun shirya kawo gyara don bude kofa ga kamfanoni masu zaman kansu don su zuba jari, ana fatan hakan kwalliya za ta biya kudin sabulu. Tsarin shi ne a inganta masana'antu yadda abubuwan da suke kerawa za su fadada izuwa nahiyar Afirka baki daya. Uwa-uba fatan shi ne samar da guraben aiki, ga dimbin matasan Afirka, wadanda ke ta gararamban neman rayuwa mai inganci a wasu kasashen na daban.

Stäcker Claus Kommentarbild App

Claus Stäcker, shugaban sashen Afirka na DW

Gwamnatin Jamus na kiyasin shigowar 'yan ci-rani daga Afirka kimanin dubu 400,000 a bana kawai. Alkaluman hasashe a yanzu na cewa izuwa sherakara ta 2030 'yan Afirka miliyan 440 za su nemi aikin yi, kuma hakan na nufin dole Afirka ta samar sabbin guraben aiki miliyan 20 a ko wace shekara, kuma samar da guraben aiki yakamata ya yi ya zarta yawan karuwar jama'an da ake samu a kasashen.

Kasashen Cote d'Ivoir, Moroko, Ruwanda, Senegal da Tunisiya, tuni suka yi alkawarin aiki da tsarin, inda suka ce zai zama, "Mu gudu tare- mu tsira tare", amatsayin Afirka da Allah ya hore ma ta yawan al'umma, hakan tuni ya nuna gamsuwarsu da shirin. Kasa kamar Jamuriyar Nijar wace karuwar al'ummarta ya rubanya har sau bakwai daga shekara ta 1960, inda rabin al'ummar kasar ke 'yan shekaru 15 da haifuwa, an jiyo shugabanta na abanton suna da jari na yawan jama'a. Don haka Nijar ta yi maraba da kawancen, inda ta ce alkaluman yawan jama'an da take da shi zai iya zama jari.

Hulda da Afirka bisa sharadi

A Jamhuriyar Nijar duk wani batun samar da wadatar abinci ba zai yi aiki ba, bisa yadda karuwar jama'a a kasar yake. Batun kayyade iyali kuwa batu ne da ba'a son jinsa a Afirka.  A taron na Berlin an amince cewa ko wace kasa tsarin da ta yi, ya kasance kansa ne za'a dora ga sabon kawancen da za'a yi, kamar dai abinda ke cikin kudurin Kungiyar Tarayyar Afirka na 2063.

A takaice dai kawai, ana nufin ba sharadi. Sabanin haka shugabannin kama karya kamar na Ruwanda, ko kuma tsarin Chaina da Afirka irin wanda Habasha ke aiwatarwa, ko wanne zai zabi yadda yake son ganin makomar kasarsa. Wannan kuwa ya samo asali ne domin kasar Jamus da Kungiyar Tarayyar Turai, suna aiki tare da shugabanni kamar na Sudan da Eritiriya a batun da ya shafi magance kwararar 'yan gudun hijira. Tsarin na Merkel na nufin ba mai fadawa Afirka abin da za su yi. Shugaba Paul Kagame na Ruwand, a a fili ma tuni ya fito ya bayyanan cewa, shi zai yi abu daban da wanda ke cikin tsarin, haka kuma shi ma shugaban kasar Ghana Akofu Ado ya ce shikam yaki da cin hanci zai baiwa fifiko, inda zai magance masu kauce wa biyan haraji.