Firiministan Slobania Miro Cerar ya ce EU na shirin wargajewa. | Labarai | DW | 25.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firiministan Slobania Miro Cerar ya ce EU na shirin wargajewa.

Miro Cerar yayi gargadin cewar kungiyar tarayyar Turai na iya daddarewa muddin dai aka kasa shawo kan matsalar 'yan kugun hijirar da ke cibaga da tsallakowa na hiyar nan da makonni masu zuwa.

Miro yace muddin kungiyar ba dauki wasu matakan gaggawa ba nan da wasu makonni dake tafe to a gaskiya kungiyar EU na iya kama hanyar wargajewa.

Kasar Slobania dai dake kasancewar karamar kasa mai yawan mutane miliyan biyu na fuskantar matsalar tsallakowar 'yan gudun hijira har sama da dubu 60.