Fataucin bangarorin jikin dan Adam na karuwa a kasashen Asiya | Labarai | DW | 07.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fataucin bangarorin jikin dan Adam na karuwa a kasashen Asiya

Kungiyar kasa da kasa akan shige da fice ta nuna damuwa game da karuwar cinikin wasu bangarori na jikin dan Adam musamman a nahiyar Asiya. Daraktan kungiyar a Asiya Bruce Reed yace fasakaurin bangarorin na jikin Bil Adam ya na karuwa a China da wasu kasashe matalauta ciki har da Kambodia, Indonesia, Laos, Burma, Filipins da kuma Vietnam. Ya ce fasakaurina fi shafan matasa. Tsarin Globalisation da ingantuwar hanyoyin sadarwa da tafiye da tafiye suna saukakawa masu fasakauri tafiyar da wannan harka da ba ta dace.