1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar madatsar ruwan Ukraine za ta kara matsalar abinci

Binta Aliyu Zurmi
June 7, 2023

Hukumar da ke samar da abinci ta duniya, ta yi gargadi kan yiwuwar samun karuwar yunwa a duniya bayan fashewar madatsar ruwa ta Kakhovka da ke kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4SJm8
Ukraine Dnipropetrovsk Regin Dnipro Fischsterben nach Dammbruch
Hoto: Cover-Images/IMAGO

Fashewar dam din da yanzu haka ya janyo ambaliyar ruwa a yankunan da ke kusa da ita, ta shafe gonaki da ba a jima da yi musu sabbin shuka ba.

Hukumar ta MDD ta ce sama da mutum miliyan 340 ne wannan ambaliyar ka iya lalatawa abinci a fadin duniya, wadanda ke dogaro kacokam ga hatsin kasar ta Ukraine.

Mahukuntan Ukraine na ganin wannan ambaliyar ka iya isa ga wasu gonakai sama da kadada dubu 10 a yankunan Dnipro da Kherson

Can ma a yankunan da Rasha ta karbe iko tuni ambaliyar ta raba mutane da dama da matsugunnansu.

Rasha da Ukraine na ci gaba da nuna yatsa a junansu a kan wanda ya yi sanadiyar ballewar ruwan, da dukkanin su ke ji a jika.