Farmaki kan ′yan Boko Haram a Sambisa | Labarai | DW | 19.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farmaki kan 'yan Boko Haram a Sambisa

Sojojin Najieriya sun ce sun hallaka mayakan Boko Haram da yawa a farmakin da suka kai ta sama a dajin Sambisa da garin Gwoza a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yuwun rundunar sojin Manjo Janar Chris Olukolade ya ce hare-haren da suka kai ta sama sun yi nasara matuka musamman ma a dajin na Sambisa idan kungiyar ke da sansanoni.

A 'yan kwanakin da suka gabata sojin na Najeriya sun ce sun hallaka 'yan kungiyar kimanin 300 a samamen da suka kai garururwa da dama inda suka karbe iko da su daidai lokacin da takwarorinsu da ke yakar kungiyar a Chadi da Kamaru da Nijar su ma suke bada labarin samun nasara a yakin da aka daura da Boko Haram din.