Farkon sakamakon zaɓe daga jihar Virginia, na nuna cewa ’yan jam’iyyar Democrats sun sake samun rinjayi a majalisar dattijan Amirka. | Labarai | DW | 09.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farkon sakamakon zaɓe daga jihar Virginia, na nuna cewa ’yan jam’iyyar Democrats sun sake samun rinjayi a majalisar dattijan Amirka.

Ban da gagarumar nasarar da jam’iyyar Democrats ta samu, ta mamaye majalisar mashawartan Amirka, a zaɓen majalisun ƙasar da aka gudanar a ran talatar da ta wuce, alƙaluman baya-bayan nan na nuna cewa, bisa dukkan jam’iyyar ce kuma za ta sami rinjayi a majalisar dattijan ƙasar. Rahotannin da muka samu ɗazu-ɗazun nan na nuna cewa jam’iyyar Democrats ɗin ce ke kan gaba, a ƙuri’un da aka ƙiga a jihar Virginiya kawo yanzu. Bisa wani ƙiyasin da gidajen talabijin ɗin NBC da CBS suka yi dai, ɗan takaran jam’iyyar Democrats Jim Webb ne ya lashe zaɓen wannan jihar. Sai dai ana raɗe-raɗin cewa, abokin hamayyarsa George Allen na jam’iyyar republicans, zai ƙalubalanci sakamakon da neman a sake ƙirga ƙuri’un.

Da yake mai da martani ga labarin nasarar samun rinjayi a majalisun ƙasar guda biyu, shugaban jam’iyyar Democrats ɗin a majalisar dattijan Amirka, Senata Larry Reid, ya ce a shirye jam’iyyarsa take ta sake wa Amirka alƙiblarta.