Fargabar yakin basasa tsakanin Kurdawa | Labarai | DW | 16.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fargabar yakin basasa tsakanin Kurdawa

Turkiya ta yi gargadin barkewar yakin basasa.Idan Kurdawa suka ci gaba da yunkurin ballewa daga Bagadaza

Ministan harkokin wajen Turkya Mevlut Cavusolgu ya yi kashedin barkewar yakin basasa idan gwamnatin yankin Kurdawa a arewacin Iraqi ya ci gaba da shirin gudanar da kuri'ar raba gardama na ballewa daga Bagadaza domin ayyana yancin cin gashin kai.

Turkiyar wadda ke da Kurdawa yan tsiraru ta na kakkausar adawa da kuri'ar raba gardamar.

Shi ma dai Firaministan Iraki Haider al Abadi yana adawa da matakin kuma yanzu haka yana tattaunawa da bangarori daban daban domin tabbatar da cigaban kasar a matsayin kasa daya dunkulalliya.