Fargabar ci gaba da yaduwar makamai a yakin Libiya | Labarai | DW | 29.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fargabar ci gaba da yaduwar makamai a yakin Libiya

Shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya bayyana fargabar yaduwar makamai zuwa wasu kasashen yankin Sahel, muddin kungiyar tarayyar Afirka AU ta gaza daukar matakan gaggawa na kawo karshen yaki a Libiya.

Da yake jawabi yayin ganawarsa da Shugaban kasar Turkiyya Raccep Tayyip Erdogan a Dakar babban birnin kasar Senegal, Shugaba Macky Sall ya ce ilahirin nahiyar Afirka na cikin damuwa kan yadda ake gwabza fada a Libiya.

Shugaban na Senegal ya bukaci daukacin kasashen Afirka su samar da mafita kan halin da Libiya ke ciki, yayin ganawar da za su yi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Kasar Libiya na cikin rudani tun 2011 bayan kashe tsohon Shugaban kasar Kanar Moamar Gaddafi, inda ake yaki tsakanin gwamnatin hadin kan kasa da duniya ta amince da ita, wadda kuma Turkiyyar ke marawa baya da madugun adawa janar Khalifa Haftar kan iko da babban birnin kasar Tripoli.