1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fargabar barkewar yaki tsakanin Ruwanda da Kwango

February 21, 2024

Amurka ta gargadi kasashen Ruwanda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da su gujewa hadarin fadawa cikin yaki bayan barkewar kazamin tashin hankali a baya-bayan nan a Gabashin Kwangon.

https://p.dw.com/p/4cdlB
Fargabar barkewar yaki tsakanin Ruwanda da Kwango
Fargabar barkewar yaki tsakanin Ruwanda da KwangoHoto: GLODY MURHABAZI/AFP via Getty Images

A yayin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinki Duniya da aka gudanar a ranar Talata mataimakin jakadan Amurka a majalisar ya ce dole ne kasashen duniya su dauki matakin gaggawa don kawo karshen fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnatin Kwango da 'yan tawayen M23 da fadar Kinshasa ke zargin suna samun goyon baya daga Ruwanda mai makwabtaka.

A baya-bayan nan dai tashin hankali na kara yin kamari a Lardin Arewacin Kivu inda 'yan tawayen M23 suka kaddamar da wani sabon farmaki tare da kai hari da jirage marasa matuka a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Goma, harin da Kinshasa ta dora alhakinsa a kan Kigali.

To sai dai ba tare da ansa wannan zargi kai tsaye ba, jakadan Ruwanda a Majalisar Dinkin Duniya Ernest Rwamucyo ya ce kasarsa za ta ci gaba da mayar da martani ga barazanar Kwango yana mai zarginta fadar mulki ta Kinshasa da taimaka wa kugiyoyin 'yan bindiga masu adawa da fadar Kigali.