1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Kwango: Sabon rikici a arewacin Kivu

Abdourahamane Hassane
February 14, 2024

A Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango an samun asarar rayuka da jikkatar fararen hula a garin Sake da ke lardin Kivu ta Arewa inda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin 'yan tawayen M23 da sojojin gwamnati.

https://p.dw.com/p/4cOTw
Kwango | Sojin kungiyar 'yan tawaye ta M23
Kwango | Sojin kungiyar 'yan tawaye ta M23 Hoto: Arlette Bashizi/REUTERS

'Yan tawayen kungiyar M23 sun kai hari sansanin ‘yan gudun hijira na Zaïna da ke kusa da garin Sake wanda ke da nisan kilomita 20 daga garin goma. Innocent  ​​​​Lukoo na daya daga cikin 'yan uwan wadanda harin ya ritsa da su

"Ina tsaye kusa da titin na ga mutane suna fita da jakunkuna, sai  na ji karar fashewar wasu abubuwa, na garzaya cikin sansanin, sai na ga a nan ne fashewar ta faru, nan take muka fara tayar da mutanen da suka ji rauni har ma akwai wadanda suka mutu, na yi mamakin ganin yar uwata wadda ta samu munanan raunuka, saboda wannan fargaba ne muka gudu domin mu zo nan Goma."

Karin Bayani: Kwango: Fada ya barke a Arewacin Kivu

Kwango | Wani soja na kungiyar 'yan tawayen M23
Kwango | Wani soja na kungiyar 'yan tawayen M23 Hoto: Arlette Bashizi/REUTERS

Kimanin mutane goma ne suka jikkata sannan uku suka mutu. Kusan dukkan mazaunan Sake sun ficce daga garin sun fake a Goma, kamar yadda Sylvie Bandux, wata uwa da ta tsira daga harin a lokacin da take kan hanyarta ta ficewa daga garin

"Na dauki haiwa da iri na shuka wake domin in je gona, amma a hanya aka tare ni, sai aka ce mini al'amarin ya kara ta'azzara a garin, da na isa gida sai kawai na dauki ‘ya'yana muka fita, muka kama hanyar ficewa daga garin yara sun galabaita a kan hanyarmu ta zuwa Goma''

Tun ranar Litinin ‘yan tawayen na M23 ke neman karbe iko da garin na Sake, amma sojojin Kwango da ke samun goyon bayan sojojin sa kai Wazalendo na kokarin dakilesu kamar yadda William Habamung dan fafutuka na kungiyoyin farar hula ya tabbatar

Karin Bayani: Daruruwan mutane sun mutu a Kwango

"A yanzu  makiya 'yan tawayen sun ci gaba da yawa daga matsuguninsu na Karuba zuwa birnin Sake, yanzu haka suna cikin Rutobogo da kuma kusa da turken wayar sadarwa, Daga ko'ina kana jin karar bindigogi amma Wazalendo sojojin sa kai da wasu sojojin gwamnatin na nan a cikin garin har yanzu''.

Garin Bukavu a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyyar Kwango
Garin Bukavu a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyyar KwangoHoto: ALEXIS HUGUET/AFP via Getty Images

Idan har birnin na Sake ya fada hannun 'yan tawayen M23, to birnin Goma zai samu kansa a ware daga sauran sassan kasar. Mafita daya tilo da za a samar wa  birnin da kayan abincin sai an tsallaka ta tafkin Kivu hakan kuwa wani rashin nasara ce na sojojin gwamnatin

Tun daga karshen shekarar 2021, lardin Kivu ta Arewa ya fada cikin rikici tsakanin kungiyar M23 da ke samun goyon bayan sassan sojojin Rwanda, da kuma sojojin Kwango masu samu goyon bayan wasu kungiyoyin da ke dauke da makamai da wasu kamfanonin sojan kasashen haya na waje guda biyu.

Kwangio na zargin Ruwanda da ‘yan tawayen M23 da neman karbe ikon ma'adinan gabashin Kongo. A nata bangaren, kungiyar M23, ta yi ikirarin kare wani bangare na al'ummar kasar da ke fuskantar barazana da wariya, kuma tana neman tattaunawa, wanda Kinshasa ta ki amincewa, kan cewar yan ta'adda ne